1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta yarda da ƙarin takunkumi ga Iran

Halimatu AbbasJuly 26, 2010

Ƙasashen Turai sun daideta kan aza wa Iran ƙarin takunkumi

https://p.dw.com/p/OVDS
Catherine Ashton, kantomar EU kan manufofin ƙetare. )Hoto: AP

Kwamishiniyar harkokin waje ta Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) Cathrine Ashton, ta ce a shirye Turai take ta duba tayin da Iran ta gabatar na sake zama teburin tattaunawa akan shirinta na nukiliya, muddin dai za ta bi hanyoyin da suka dace. Ashton ta na mai da martani ne ɗazu a birnin Brussels, bayan samun labarin niyyar Iran ta sake zama teburin sulhu da ƙasashen na duniya. A ɗazu ne dai ƙungiyar ta EU ta amince da ƙarin takunkumi akan ƙasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukiliya. A wani taro da ministocin harkokin wajen ƙasashen na Turai suka gudanar yau Litinin a birnin Brussels, sun ce ƙarin takunkumin ya shafi kasuwanci na ƙasa da ƙasa da man fetur da kuma iskar gas da Iran ke fitarwa zuwa ƙetare. Wannan ƙarin takunkumin da Turawan yamman suka ƙaƙaba akan Iran dai, ƙari ne akan wanda Majalisar Ɗinkin Duniya(MƊD) da Amirka suka ƙaƙaba wa ƙasar, a ƙoƙarin da suke yi na ganin Iran ta dakatar da shirinta na inganta sinadaran makamashin nukiliya da kuma sake komawa teburin sulhu da ƙasashen duniya.

Mawallafi: Babangida Salihu Jibril

Edita: Halima Balaraba Abbas