1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta yi wa Google tarar biliyoyin euro

June 27, 2017

Hukumar EU mai karfin iko kan gogayyar cinikayya ta yi wa kamfanin fasaha na Google tara mai tsoka domin ladabtarwa kan saba dokokin gogayyar cinikayya.

https://p.dw.com/p/2fTnN
Google startet 'right to be forgotten' Formular für Entfernung von Inhalten
Hoto: picture-alliance/ROPI/Eidon/Scavuzzo

Hukumar da ke sa ido kan gogayyar cinikayya ta kungiyar tarayyar Turai ta yi wa kamfanin fasaha na Google tarar euro biliyan biyu da miliyan dari hudu, kan abin da ta kira rashin adalcin kamfanin wajen gogayya da sauran kamfanoni irinsa.

Da ta ke baiyana hukuncin kwamishiniyar tarayyar Turai mai kula da gogayyar cinikayya Margrethe Vestager ta ce kamfanin na Google ya hana sauran kamfanoni rawar gaban hantsi.

Ta ce hukumar ta yi wa Google tarar euro biliyan biyu da miliyan dari hudu saboda keta dokokin kungiyar tarayyar Turai na gogayyar cinikayya. Google ya keta dokokin kasuwanci tare da fifita wani bangare na hajjarsa ta harmtacciyar hanya akan sauran kamfanoni.

Hukumar gogayyar cinikayyar ta kungiyar tarayyar Turai ta kuma baiwa kamfanin na Google wa'adin kwanaki 90 ya dakatar da wannan halayya ko kuma ya fuskanci biyan tara mai yawa.