1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Taro a kan rikicin cikin gida na Rasha

June 26, 2023

Ana sa ran, tawayen da sojojin Wagner suka yi a Rasha ya mamaye zauren taron ministocin harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai da zai gudana a Luxembourg.

https://p.dw.com/p/4T3Nv
Hoto: European Union

A karshen mako ne dai babban jami'in harkokin kasashen ketare na EU, Josep Borell ya gana da takwarorinsa na kungiyar yayin da sojojin hayar Rasha na Wagner suka tunkari Moscow da nufin hambarar da shugabancin sojojin Rasha, kafin daga bisani su janye.

Taron na wannan Litinin din da zai samu halarcin ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ta kafar bidiyo, ministocin za su kara jadadda goyon bayansu ga gwamnatin Kyiv da kuma aniyarsu na sake bata tallafin harsasai miliyan daya da kuma shirin horas da dakarun Ukraine kimanin dubu 24 nan da karshen wannan shekarar.

Taron zai kuma tattauna batun takun sakar kasashen Kosovo da Serbiya da ma batun rikicin Armeniya da Azerbaijan ko ba ya ga halin da ake ciki a Tunusiya. Ta yiwu, ministocin su sake kakaba takunkumi ga kasar Iran bisa ci gaba da take hakkin bil Adama.