1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Taro domin taimakon Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
April 25, 2018

Kungiyar Tarayyar Turai EU, ta bukaci kasashen Rasha da Iran da kuma Turkiya da su tabbatar da ganin an kawo karshen yakin da ake a Siriya.

https://p.dw.com/p/2weFN
Syrien-Geberkonferenz in Brüssel
Mahalarta taron samar da gudunmawa ga SiriyaHoto: Getty Images/AFP/E. Dunand

Wannan kira dai na zauwa ne a dai-dai lokacin da al'ummomin kasa da kasa ke gudanar da wani taro a birnin Brussels na kasar Beljiyam da nufin samar da kudin tallafi ga kasar da yaki ya dai-daita. Yakin na Siriya da ke shiga shekararsa ta takwas dai, yayi sanadiyyar asarar rayukan al'ummar Siriya sama da miliyan 13 yayin da wasu sama da miliyan biyar ke yin gudun hijira. Da take jawabi a yayin wannan taro da ke gudana da hadin gwiwar Majalaisar Dinkin Duniya, shugabar hulda da kasashen ketare ta kungiyar Tarayyar Turan, Federica Mogherini ta nunar da cewa kasashen uku na Rasha da Iran da kuma Turkiyya na da nauyi na musamman a kansu na ganin an tsagaita wuta, kana su tabbatar da dawo da wakilan gwamanatin Shugaba Bashar al-Assad kan teburin sulhu.

Da take jawabi kan taron da kuwa Mogherini  cewa ta yi kungiyar Tarayyar Turai za ta tabbatar da gudunmawar da aka samu kamar shekarar da ta gabata, kuma za su ci gaba da gudanar da wannan taro duk shekara domin samar da gudun mawa ga Siriya har nan da shekara ta 2020. A nata bangaren Jamus ta sanar da gudunmawarta ta zunzurutun kudi Euro biliyan guda ga al'ummar Siriya da ke gudun hijira a kasashe makwabta da ma wadanda ke cikin kasar.