1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tashi ba cimma matsaya a taron EU

Abdoulaye Mamane Amadou
July 20, 2020

Shugabanni da hukumomi membobin kungiyar tarayyar Turai za su sake komawa kan teburin tattauna batun farfado da tattalin arzikin kasashen, biyo bayan da aka tashi dutsi hannun riga a taron.

https://p.dw.com/p/3fZyf
EU-Sondergipfel zur Bewältigung der Corona-Wirtschaftskrise
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/Reuters Pool/F. Lenoir

An shafe tsakiyar daren jiya zuwa ranar Litinin ana mahawara kan batun adadin kudaden da takamata a ware don shawo kan matsalolin tattalin arzikin da kasashen suke fuskanta. Tun daga farko kasashen 27 sun kasa cimma wata matsaya ne kan adadin kudaden da za su ware a matsayin tallafi. Kasashen sun samu rarrabuwar kawuna wajen amince da kaso n kudaden da za a ware.