1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na taron duba sabon shirin farfado da tattalin arziki

Abdoulaye Mamane Amadou
July 17, 2020

Shugabanni da hukumomin kasashe membobin kungiyar tarayyar Turai za su gana a yayin wani taron koli irinsa na farko tun bayan bullar annobar corona don duba batun farfado da tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/3fSOx
Brüssel Europäische Kommission Außenansicht
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Kalker

Ana sa ran taron zai cimma matsaya kan batun tsarin nan na sake farfado da tattalin arzikin kasashen da ya tanadi Euro miliyan dubu 750, inda ciki sabon shirin za a ware wasu kudi a matsayin bashi da kuma wasu a matsayin tallafi daga kasashen da suka kimanin Euro miliyan dubu 500.

Masu aiko da rahotanni sun ce akwai yiwuwar tafka muhawara mai zafin gaske kafin shugabannin su cimma wata yarjejeniya kan sabon shirin, duba da yadda wasu kasashen ke nuna dari-dari kan batun, duk da yake yana daya daga cikin tsarin farfado da tattalin arzikin yankin na shekarar 2021 zuwa 2027 da ya haura Euro biliyan dubu daya.