1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma matasaya kan bakin haure

Abdoulaye Mamane Amadou
July 31, 2019

Kungiyar Tarayyar Turai ta cimma wata matsaya kan batun karbar bakin haure 131 da aka ceto daga teku, wadanda suka jima makale a jirgin ruwan Italiyan da ya cecesu Gregoretti sakamakon kin karbarsu daga kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/3N5Yc
Mittelmeer: Rettung von Flüchtlingen in Seenot
Hoto: picture-alliance/L. Schmid/SOS Mediterranee

Kasashen Faransa Jamus Portigal Luxemburg da Irland, tare da tallafin Cocin Italiya ne suka cimma wannan yarjejeniya a yau Laraba, a wani yunkuri na kawo dauki ga bakin hauren 131, da suka jima suna gararamba a cikin jirgin a gabar tekun Sicile na Italiya ba tare da wata kasa ta karbesu ba.  

Duk da yake ya zuwa yanzu kungiyar bata fayyace yadda za a rarraba adadin bakin hauren ba, rahotanni sun ce galibin bakin hauren da aka ceton za su kasance ne a kasar Italiya inda babbar Cocin kasar za ta dauki nauyinsu.