EU: Barazanar hana fitar da AstzraZeneca waje
March 20, 2021Talla
Wannan na zuwa ne a yayin da lamura ke kara ta'azzarar saboda jinkiri wajen jigilar allurarrigakafin da ya janyo tashin tashina tsakanin kasashen.
Ta ce kungiyar EU na da zabin haramta shirin fitar da alluran zuwa wasu kasashe. Wannan sako ne zuwa ga AstraZeneca. Wajibi ne kamfanin ya fara cikanta yarjejeniyarsa da Turai, kafin kai wa wasu kasashe.
Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Turan ke fafutukar gaggauta yin allurar COVID 19 wa al'umma, a yayin da kasashen nahiyar da dama ke cikin wadi na tsaka mai wuya dangane da kara yaduwar cutar.
A cewar von der Leyen kamfanin AstraZeneca ya bada kashi 30 ne kacal daga cikin allurai miliyan 90 da ya yi alkawarin bayarwa a watannin ukun farko na wannan shekara.