1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta aiwatar da takunkumin MDD a kan Iran

February 12, 2007
https://p.dw.com/p/BuRz

A karshen taron su a birnin Brussels, ministocin harkokin waje na ƙungiyar tarayyar turai sun amince da aiwatar da takunkumin majalisar ɗinkin duniya a kan ƙasar Iran, sai dai kuma sun ƙi bada goyon baya ga buƙatar Amurka da Britaniya na ɗaukar matakai masu tsauri a kan ƙasar ta Iran. A cikin watan Disambar bara ne dai majalisar ɗinkin duniyar ta sanyawa Iran matakin farko na takunkumin karya tattalin arziki sakamakon gazawar ta na bada tabbatacciyar shaidar cewa shirin na nukiliya na lumana ne kamar yadda ta yi iƙrari. A hannu guda Amurka ta soki lamirin tarayyar turai da cijewa wajen gaggauta aiwatar da takunkumin. Takunkumin dai ya haɗa da haramta musayar muhimman sinadarn nukiliya ga Iran da rike kadarorin mutanen dake da alaƙa da shirin makamashin nukiliyar tare kuma da buƙatar ƙasashe su bayar da bayanai a game da mutanen dake cikin jadawalin sunayen da majalisar ɗinkin duniyar ta gabatar.