1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta bada izinin shiga ga masu rigakafi

Abdullahi Tanko Bala
May 19, 2021

Kasashen kungiyar tarayyar Turai sun amince za su sassauta tarnaki kan tafiye tafiye ga maziyarta daga kasashen da ba na turai ba amma sai wadanda aka yiwa allurar rigakafdin corona.

https://p.dw.com/p/3tcz0
Einreise EU | Covid-19: Airport Corona Testing
Hoto: Zumapress/picture alliance

Jakadun kasashen 27 na EU sun amince da wasu sharwari da hukumar tarayyar Turan ta gabatar a ranar 3 ga watan Mayu domin sassauta tarnaki ga wadanda aka yiwa allurar rigakafi don basu damar ziyarar bude ido.

A wannan makon ake sa ran kasashen za su gabatar da shawarwarin bisa jadawalin bayanai daga cibiyar yaki da cutattuka masu yaduwa musamman ga mutanen da za su shigo daga Birtaniya.

Sai dai wani jami'in diflomasiyyar yace akwai bukatar nazari sosai akan nau'in cutar da aka samu a Indiya wanda ya bulla a Birtaniya.

A karkashin dokar da ake da ita a yanzu mutane daga kasashe bakwai ne kawai da suka hada da Australia da Israila da Singapore aka amincewa shiga kasashen EU yayin da ba a amincewa sauran kasashen ba ko da kuwa sun yi allurar rigakafin.