1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta kakabawa wasu jami'an kasar Iran takunkumai

Binta Aliyu Zurmi
October 19, 2022

Kungiyar tarayyar Turai ta amince da kakaba takunkumi kan wasu mutane 8 da kungiyoyi saboda amfani da jirage marasa matuka kirar Iran, wanda Rasha ta yi amfani da su wajen kai wasu hare-hare a kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4IQCm
Flagge Iran und EU
Hoto: Zoonar/picture alliance

Kwararru a kan takunkumai na kasashen EU 27 sun amince da jerin wadanda matakin zai hau kansu a wani taro da suka gudanar a yau.

Ya zuwa gobe Alhamis ne dai a ke sa ran gwamnatocin na EU za su amince da kudirin kakaba takunkumin, gabanin taron da da za su gudanar na yini biyu a birnin Brussels din Benjium.

Iran da ake shirin ladabtarwa a kan amfani da makamanta da Rasha ta yi ta musanta hakan, saa nata bangaren Rasha bata ce uffan ba. 

Sai dai ko a jiya kamfanin dillancin labarai na Reuters ya sanar da cewar Iran ta yi alkawarin samarwa da Rasha wasu makamai masu linzami kari a kan wadannan jirage da ake zarginta da samarwa.