EU za ta kara kudin tallafa wa 'yan gudun hijira
September 23, 2015Shugabannin kasashen Turai 28 mambobin Kungiyar Tarayyar Turai sun sha alwashin samar da karin wasu kudaden miliyon dubu na Euro ga kungiyoyin agaji na MDD masu tallafa wa 'yan gudun hijira a kasashe makwabtan Siriya irinsu Turkiyya Jodan da Lebanan. Kasashen sun dauki wannan mataki ne a taron koli na shugabannin nasu da ya gudana a wannan Laraba a birnin Brussels.
Da ya ke jawabi a gaban manema labarai shugaban hukumar zartarwar kungiyar ta EU Donald Tusk ya ce a halin yanzu za a iya cewar sun cimma matsaya a game da muhimman batutuwan da suka jima suna haifar da zarge-zarge tsakanin kasashen nasu. Sai dai ya ce babban kalunalen da a halin yanzu ya yi wa kasashen asu saura shi ne na shawo kan matsalar tsaron iyakokin waje na kasashen.