Rasha: EU ta umurci mambobinta su rage shan gas
July 20, 2022Talla
Hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta wallafa wasu dabaru na gaggawa da take sa ran tunkarar matsalar karancin makamashi a kasashen kungiyar. Shugabar hukumar Ursula von der Leyen ta zargi Rasha da amfani da batun makamashin a matsayin sandar duka domin mayar da martani kan takunkuman da aka sanya mata biyo bayan mamayar da take yi wa Ukraine.
Daga cikin dabarun da EU ta fitar, kungiyar, ta bukaci mambobinta su rage kaso 15 cikin 100 na makamashin iskar gas da suke amfani da shi a lokacin hunturu tsakanin watan Agusta zuwa Afrilu.