1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta taka rawa a yankin gabas ta tsakiya

October 11, 2010

Tarayyar Turai ta fara ɗaukar matakai na sasanta rikicin Isra'ila da Palsɗinawa, wanda yake neman rugujewa.

https://p.dw.com/p/Pc2y
Mahmoud Abbas yake bayani wa Bernard KouchnerHoto: AP

Ƙasashen Tarayyar Turai sun bayyana anniyar su ta ci gaba da taka rawa don warware rikicin gabas ta tsakiya, duk kuwa da kalaman ranin wayo da ministan harkokin wajen Isra'ila ya yi musu. Ministan harkokin wajen Faransa Bernerd Kouchner da takwaransa na ƙasar Spain, waɗanda suka wakilci ƙasashen EU 27, sun gana da Firai minista Benjamen Netanyahu da ministan harkoin wajen Isra'ila Lieberman, wanda yace ƙasashen na Tarayyar Turai da su warware rikicin dake gidansu, kafin suce za su yi katsalanda a harkar gabas ta tsakiya. Bayan ganawarsu da mahukuntan Isra'ila a yau, ministocin na EU sun shige ƙasar Jodan inda suka gana da Sarki Abdallah, kana daga bisani suka tattauna da shugaban Palasɗinu Mahmud Abbas a keɓe. Tarayyar Turai dai tana son nuna rawarda za ta iya takawa don raya tattaunawar ƙeƙe da ƙeƙe da aka fara tsaknin Palasdinawa da Yahudawa. Tattaunawa da yanzu ta shiga halin rashin tabbas, bayan da Isra'ila ta yanke shawar ci gaba da ginawa Yahudawa gidaje a yankunan Larabawan da ta ƙwace.

Mwallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tanko Bala