Ci gaba da tallafa wa 'yan gudun hijira a Turkiyya
March 25, 2021Talla
A taron da suka gudanar shugabannin sun ce abu mafi mahimmanci a wannan lokaci shi ne dafa wa Turkiyya domin ta ci gaba da kula da dubban 'yan gudun hijirar da ke jibge a kasarta maimakon yi mata baraza da matakin kakaba mata takunkumi.
Yanzu haka EU ta sha alwashin farfado da tsohuwar jarjejeniyar da suka cimma a shekarar 2016, yarjejeniyar da ta dakile tururuwar da 'yan gudun hijirar kasar Siriya ke yi a gabar tekun kasar Girka.
Babban jami'in harkokin ketare na Kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce ya zama wajibi EU ta ci gaba da ba wa Turkiyya zunzurutun kudi har yuro biliyan shida domin ci gaba da kula da 'yan gudun hijirar da ke jibge a kasarta.