EU za ta yaki masu safarar mutane a teku
May 18, 2015Kungiyar tarayyar Turai ta EU na shirin gudanar da wani zama na musamman a yau(Litinin) domin fito da wani shiri na yaki da safarar mutane zuwa kasashen Turai.Wanan shiri na da nufin tanadar jiragen yaki da na'urorin bincike da za a girke a gabar ruwan kasar Libiya da ta kasance babbar kofar da bakin hauren ke bi domin zuwa kasashen na Turai.
Sai dai wannan shiri na bukatar amincewar Majalissar Dinkin Duniya, kuma sai a cikin watan Yunin ne zai fara aiki gadan-gadan. Ministocin kula da harakokin kasashen waje na kasashen 28 na Turai za su halarci taron tsara wanann shiri a birnin Bruxelles bayan wata ganawa da za su yi da ministocin kula da harkokin tsaro na kasashen nasu.
Kantomar kungiyar tarayyar Turai kan manufofin ketare Federica Mogherini ta ce Shirin na da burin bankado kungiyoyin masu safarar bakin hauren domin karya lagwansu dama gurfanar da shugabanninsu a gaban kuliya. Sannan ta na zama wata amsa ga zargin da wasu kasashen duniya ke yi ma EU na nuna sakaci ga matsalar mutuwar bakin hauren a cikin teku da sahara a kokarinsu na neman tudun mun tsira a kasashen nasu.