Najeriya: Kungiyoyin duniya sun bayar da sabanin ra'ayoyi
February 25, 2019A wani rahoton da wallafa game da babban zaben Najeriya Kungiyar Tarayyar Turai da wakilanta da suka sanya ido kan yadda aka gudanar da zabe a ranakun Asabar da Lahadi ta bayyana damuwa da wasu kurakurai da aka samu a yayin gudanar da zaben, da suka hada da cin zarafi da tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar.
Rahoton da tawagar ta bayyana a wannan Litinin din a Abuja, kungiyar ta ce an bude mafi yawan rumfuna zabe a makare saboda rashin kayan aiki, kana babu wasu cikakkun bayyanai ko za a kara lokacin ci gaba da kada kuri'a ko akasin haka, lamarin da ya haifar da rudani ga masu zabe.
Kungiyar Tarayyar Turan ta ce akwai bukatar kawo gyara a zaben gwamnonin da ke tafe. Kungiyar ta soki lamirin zaben ne a daidai lokacin da kungiyar kasashe renon Ingila ta ce ta gamsu da yadda zaben ya gudana musamman wajen damar da aka baiwa masu bukata ta musamman.
Mai magana da yawun kungiyar ta kasashe renon Ingila (Commonwealth) Tsohon shugaban kasar Tanzaniyya Jakaya Kikwete, ya bayyana zaben da cewa abin yabawa ne, yana mai cewa an samu ci gaba. Ana ta bangare cibiyar raya dimukradiyya da ci-gaban kasa ta Najeriya (CDD) ta fitar da nata rahoton game da zabe tare da bayyana kurakuran da ta lura sun wakana tana mai cewa akwai bukatar kawo gyara a zaben da ke tafe.