Euro 2022: Wadanda aka fi sa wa ido
Yayin da ake gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Turai bangaren mata a Ingila, wadannan su ne kasashen da ake sa ran za su taka rawa da kuma fitattun 'yan wasansu.
Jamus
Tawagar Martina Voss-Tecklenburg tana cike da 'yan wasa daga manyan kungiyoyin Turai. Jamus za ta yi la'akari da hadin kai tsakanin matasa da kwararrun mata, burin Hukumar Kwallon Kafa ta Jamus (DFB) shi ne akalla wasan kusa da na karshe. Sara Däbritz, wacce kwanan nan ta shiga zakarun Turai, Lyon, za ta yi kokarin lashe babban kambun na farko na Jamus tun 2013.
Norway
Bayan rashin jin dadin fitar da su a matakin rukuni na gasar Euro 2017, Norway za ta yi kokarin dawo da kyakkyawan tarihinta a gasar, bayan da ta lashe sau biyu kuma ta kai wasan karshe a 2013. Ada Hegerberg, wanda ta lashe kyautar Ballon d’Or ta farko ga mata a 2018, ta dawo cikin tawagar bayan shekaru biyar tana nuna adawa da rashin daidaito a cikin Hukumar Kwallon Kafa ta Norway.
Faransa
Bayan rashin tabuka abin kirki a Kofin Duniya a gida a 2019, tawagar Corinne Diacre za ta yi kokarin daidaita kanta. Hakan zai yi wuya saboda rashin fitattun 'yan wasa kamar Amandine Henry da Eugenie Le Sommer, da ba sa cikin tawagar. Kwararriyar mai tsaron baya Wendie Renard, ta Lyon da ta lashe gasar Champions League. Za ta jagoranci wata tawaga da ke da tarihin nasarori a fannin club-club.
Holland
Zakarun Turai da ke rike da kofin za su yi kokarin kare kambunsu a Ingila, a wannan karon kuma dan Ingila Mark Parsons ne ke jagorantarsu. Ana sa ran Vivianne Miedema ta Arsenal, tauraruwar 'yar wasan da ta fi zura kwallo a raga a kasar Holland, watakila za ta jagoranci kungiyar zuwa matakin karshe na gasar.
Ingila
Masu karbar bakoncin gasar na kallon kansu a matsayin daya a cikin wadanda za su yi fice. Kungiyar na da ’yan wasan gasar Super League ta mata da ke tashe cikin sauri, da kuma manyan kungiyoyin Turai. 'Yar wasan baya Lucy Bronze ta taka leda da wasu fitattun mutane, kuma za ta yi kokarin samun nasarar lashe gasar cin kofin a Ingila bayan da ta kulla yarjejeniya da Barcelona a kakar wasa mai zuwa.
Spain
Tare da tawagar da aka yi kiyasin gaba daya ta kwararrun ne a La Liga, 'yan wasan Jorge Vilda za su yi kokarin tabbatar da nasarar kasar ta farko a gasar ta Turai. 'Yar wasan Barcelona, Alexia Putellas, da mutane da yawa suka dauka a matsayin mafi kwarewar 'yar wasa a duniya, ita ce za a zubawa ido.
Sweden
Da yawa daga cikin 'yan wasansu ke zama adon kungiyoyin Turai da kuma tarihi mai karfi, Sweden na daya daga cikin kungiyoyin da za a kalla a gasar Euro. Wadanda suka samu lambar azurfa a gasar Olympics ta Beijing, za su yi kokarin lashe babban kofi a karon farko tun bayan da suka lashe gasar Euro a 1984. Ana ganin Fridolina Rolfö daga Barcelona ka iya taimaka musu wajen cimma burinsu.