Euro 2024: Gasar cin kofin nahiyar Turai
June 14, 2024Akalla baki kusan miliyan 12 ne ciki har da 'yan kallo miliyan biyu da dubu dari bakwai ake sa ran za su kasance a birane dabam-daban na Jamus daga ranar 14 ga wannan wata na Juni zuwa ranar 14 ga watan Juli domin halartar gasar kwallon kafa ta cin kofin kasashen nahiyar Turai Euro 2024.
Batun samar da ingantaccen tsaro ga tawagogin 'yan wasa daga kasashe 23 da kuma a filayen da za a yi gumurzun da za a share wata guda cur ana fafatawa na daga cikin manyan kalubalen da mai masaukin baki Jamus ta mayar da hankali a kai kamar yadda ministan cikin gida ta kasar Nancy Faeser ta sanar a baya-baya nan. Nancy ta ce baya ga filayen wasa za a karfafa bincike a tashoshin jiragen kasa da na bus-bus don ganin gasar ta gudana ba tare da wata fargaba ko barazana ba.
Baya ga batun tsaro, Filayen kwallon kafa na Jamus sun sha kwalliya ta musamman domin karbar manyan wasannin da za a fafata a lokacin gasar wace Jamus ta dade tana jira, kuma a wannan fanni Berlin ta kashe miliyoyin kudade don kawata filayen wasanni guda 10 da aka tanadar wa gasar. Daga cikin filayen wasan har da Alianz Arena na birnin Munich mai daukar 'yan kallon 75,024, kuma a nan ne ma za a yaye labulen gasar inda tawagar mai masaukin baki za ta kece raini da takwararta ta Scotland. Tuni ma dai sa'o'i kadan kafin fara karawar aka fara kadade da raye-raye har ma da gajimaren hayaki cikin launika a wannan birni da ke kudancin Jamus wanda ya cika makil da ma'abota kwallon kafa musamman magagoya bayan tawagar 'yan wasan Scotland da su yi dafifi domin kara wa wasan armashi.
"Yadda guri ya dauki harama yanayi ne mai kayatarwa sosai shi ya sa nima na zo in raya a cikin wannan dandazon jama'a. Abin birgewa ne yadda 'yan Scotland suke ta biki a nan dandalin Marien tsawon kwanaki uku ke nan, a nutse kuma cikin annashuwa. Mun amince cewa za mu yi kunne doki a wasanmu na daren yau."
Wani batu da ke daukar hankali a gasar ta bana shine wace kasa ce za ta gaji Italiya da ke rike da kofin a halin yanzu wace da kyar da jibin goshi ta samu tikitinta. To amma masu sharhi duk da cewa Jamus ta yi shiri na musamman kafin gasar, masu sharhi kan harkokin wasanni kwallon kafa irinsu Muzammil Dalha Yola daga Najeriya na bayyana kasashe biyar a matsayin wadanda da ake wa fatan za su kai labari duk da ma da akwai wasu tawagogin 'yan wasa da ka iya yin ba zata.
A maraicen wannan Juma'a kuma kasashen da ke kunshe a cikin rukunai shida za su gaba da fafatawa daga gobe Asabar a filaye guda 10 da aka tanadar. Daya daga cikin manyan karawa da ake jira, a maraicen gobe Asabar Spain za ta ceke raini da Croitia a runkunin B a birnin Berlin yayin da Italiya da ke rike da kofin za ta barje gumi da Albaniya a rukunin na B sai kuma wasa tsakanin Hungry da Switzerland a rukunin A.