Euro 2024: 'Yan wasa masu kasashe biyu
Ga 'yan wasa da dama, babu tambaya kan kasar da suka zaba idan ana batun buga wasan kwallon kafa na kasa da kasa. Ga wasu kuma abun ba a bayyane yake ba, wasu kuwa suna da zabi.
Jamal Musiala
Jamal Musiala ya fuskanci kalubale wajen zabar kasarsa ta asali Jamus ko Ingila da ya rayu tun yana da shekaru bakwai a duniya. Dan wasan rainon makaranatar koyon kwallon kafa ta Chelsea ya dawo kungiyar Bayern Munich ta Jamus, inda ya zabi Jamus duk da ya buga wasanni a matakan matasan 'yan kwallo dabam-dabam a Ingilan. Ya fara bugawa kungiyar Nationalmannschaft ta Jamus, a watan Maris na 2021.
Kylian Mbappe
Zai wahala ka yi tunanin ganin Kylian Mbappe sanye da rigar kwallon kafa ta wata kasa in ba Les Bleus ba, amma shi ma yana damar bugawa karin kasashe biyu. Zai iya buga wa Kamaru saboda mahaifinsa, zai iya zabar kungiyar Indomitable Lions. Ko kuma ya buga wa Fennec Foxes ta Aljeriya saboda mahaifiyarsa. Sai dai a Faransa kawai ya taba buga wasa, tun daga kungiyoyin 'yan wasa masu kananan shekaru.
Mateo Retegui
Za a iya cewa Mateo Retegui sabon dan wasa ne a Italiya, tun da an haife shi kuma ya girma a Ajantina. Ya fara suna sanda ya buga wa kungiyar Boca Juniors a 2018. Bayan buga wa kungiyoyin kwallon kafa uku a Ajantina ya koma kasar kakanninsa biyu Italiya, inda ya fara buga wasa a Serie A. Ganin yana da damar buga wa Italiya wasa, ya fara buga wasa a kungiyar Azzurri a watan Maris na 2023.
Callum Styles
Callum Styles bai yi kama da sunan 'yan asalin Hangari ba, sai dai kuma yana sanye ne da rigar 'yan wasan kasar. Haifaffen Greater Manchester Ingila, Styles ba lallai sai a kungiyar Three Lions kawai zai iya buga wasa ba zai ma iya zabar Ukraine kasancewar kakanninsa sun fito daga kasashen Ukraine da Hangari. Ya fara bugawa Hangari wasa, yayin wasan sada zumunci da Sabiya a watan Maris na 2022.
llkay Gündogan
Haifaffen garin Gelsenkirchen, llkay Gündogan ya fara suna a kungiyar Dortmund kafin ya koma Manchester City yanzu kuma yana Barcelona. Kafin Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Duniya ta 2018, shi da dan wasan Jamus Mesut Özil sun gana da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan. Hakan ya janyo cece-kuce a Jamus, inda Özil ya yi ritaya bayan gasar shi kuma Gündogan ya ci gaba da buga wa kasarsa Jamus.
Lamine Yamal
Lamine Yamal ya fara suna a Barcelona yana shekaru 15 da watanni tara a duniya a Afrilun 2023, watanni shida bayan nan ya fara buga wa babbar kungiyar Spaniya da shekaru 16 da kwanaki 50. Ya ci kwallo a wasansu da Jojiya da suka yi nasara da ci bakwai da daya, dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci kwallo a tarihin kasar ya zabi Spaniya a kan kasashen iyayensa na Maroko da Equatorial Guinea.
Jeremie Frimpong da Memphis Depay
Jeremie Frimpong (daga hagu) yanzu ne zai fara buga wa Jamus wasa, yayin da Memphis Depay (na biyu daga dama). Ta hanyar mahaifinsa, Memphis zai iya zabar buga wasa a Ghana. Dan asalin Amsterdam Frimpong zai iya buga wasa a Ghana ko ma zabi na uku Ingila kasancewar sun koma can da zama tun yana dan shekaru bakwai a duniya, sai dai ya zabi buga wa Jamus.
Romelu Lukaku
Da shekaru 31 a duniya, Romelu Lukaku ya yi kakar wasanni ta bana a matsayin aro a kungiyar Roma daga Chelsea. Ya fara buga wa Beljiyam a matakin 'yan kasa da shekaru 15, ya buga a babbar kungiyar kasar a wasan sada zumunta da Croatia a watan Maris na 2010. Ya zama dan wasan Beljiyam da ya fi zura kwallo da kwallaye 83 a wasanni 114. Ya zabi Beljiyam maimakon Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.
Hakan Calhanoglu
Hakan Calhanoglu dan wasan da aka haifa a Jamus da ke da asali da Turkiyya, ya yanke shawarar buga wasa a kasar iyayensa. Haifaffen Mannheim ya fara wakiltar kungiyar 'yan kasa da shekaru 16 da Turkiyya, kafin ya wakilci babbar kungiyar kasar a watan Satumbar 2013. Amma bai taba yin wasa a wata kungiyar ta Turkiyya ba, sai dai ya yi wasa a Jamus. A yanzu ya koma Serie A, yana buga wasa a Inter.
Rafael Leao
An haifi Rafael Leao a wajen birnin Lisbon na Portugal, ya kuma fara buga wasa a kungiyar Sporting CP kafin ya fara wasa a babbar kungiyar a Fabarairun 2018. Zai iya zabar kasashen Angola ko Sao Tome da Principe saboda iyayensa, sai dai mai shekaru 24 a duniyar ya wakilci kungiyoyin 'yan wasa masu kananan shekaru na Portugal dabam-dabam kafin fara wakiltar babbar kungiyar kasar a Oktoban 2021.
Josip Stanisic
Josip Stanisic (a dama) babban misali na Jamusawa da bakin ma'aikata daga tsohuwar Yugoslabiya suka haifa. Ya fuskanci kalubale, kafin ya zabi kasar da zai wakilta. Stanisic ya buga wasanni biyu ga kungiyar 'yan kasa da shekaru 19, amma da ya kai matakin 'yan kasa da shekaru 21 ya sauya ra'ayi. A shekara ta 2021, ya fara wakiltar babbar kungiyar kasar iyayensa Kuroshiya a yanzu.
Granit Xhaka and Xherdan Shaqiri
Granit Xhaka da Xherdan Shaqiri sun buga wasanni sama da 120 ga Switzerland, kuma duka sun fara ne daga garin Basel. Dukansu za su iya wakilitar Albaniya, kamar dan uwan Granit wato Taulant saboda asalin da sauke da shi da Kosovo da Albaniya. Kai a nan ma aka haifi Shaqiri. Bayan an amince da Kosovo a UEFA da FIFA a 2016, 'yan wasan sun samu kasa ta uku da suke da zabi.