1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗi tashin harkokin siyasa a Pakistan

Ibrahim SaniDecember 10, 2007
https://p.dw.com/p/CZY3

Jam´iyyar tsohon Faraministan Pakistan, Nawaz Sharif ta bayar da sanarwar shiga zaɓen gama gari da ake shirin gudanarwa a ƙasar. Ɗaukar matakin ya zo ne bayan da Jam´Iyyar ta Mr Nawaz ta gaza shawo kan Jam´iyyar Benazir Bhutto ƙauracewa wannan zaɓe ne. Hasashen ragowar Jam´iyyun adawa na ƙauracewa zaɓen a yanzu haka ya kwanta dama, bayan ɗaukar matakin shiga zaɓen daga manya-manyan Jam´iyyun adawa na ƙasar guda biyu. Jam´iyyun adawa na zargin Mr Musharraf da shirye-shiryen gudanar da maguɗi a zaɓen na ranar 8 ga watan Janairun shekara ta 2008. Ɗaya daga cikin hujjojin da su ka bayar shi ne na ci gaba da kasancewar dokar ta ɓaci a ƙasar. Mr Musharraf ya ce za a ɗage dokar ta ɓacin kafin zuwan ranar da aka shirya gudanar da zaɓen na gama gari.