faɗuwar jirgin sama a ƙasar Pakistan
April 20, 2012Talla
A ƙasar Pakistan, wani jirgin sama da ke ɗauke da fasinjoji 130 ya faɗi a kusa da Islamabad babban birni a yammaci juma'a sakamakon rashin kyaun yanayi da ya fiskanta. Wani babban jami'an 'yan sanda na wannan ƙasa ta Asiya ya nunar da cewar jirgin ya ƙone ƙurmus, Kana ba wanda aka tsamo da ransa ya zuwa yanzu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Pakistan ke fiskantar haɗarin jirgin sama a shekarun baya-bayannan ba. Ko da a watan julin 2010, sai da wani Airbus ya faɗi a tsaunukan Margalla tare da salwantar da rayukan mutane kimanin 152.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar