Faɗuwar kuɗin Euro
May 18, 2010Talla
Ƙasar Jamus tana matsawa takwarorin ta masu anfani da kuɗin euro, da su gaggauta cike giɓin kasafin kuɗin dake kansu, don ceto darajar takardar ta euro, wanda rigimar ƙasar Girka ta yiwa lahani. Ministan kuɗin ƙasar Wolfgang Schäuble ya shaidawa masu aiko da rohotanni a taron ministocin da ake yi a Burassel cewa, cike giɓin shine kaɗai ko wacce ƙasa za ta yi, ta ceci kanta da sauran ƙasashe. A jiya dai darajar kuɗin euro ta yi faɗuwar da bata yi ba tun shekaru huɗu da suka gabata. Shugaban ƙungiyar ƙasashen da ke anfani da kuɗin euro Jean-Claude Juncker, yace ya damu sosai yadda faɗuwar euron yake ƙaruwa kamar wutar daji.
Maqwallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu