Kamfanonin China sun yi wa Facebook kutse
June 6, 2018Talla
Kamfanin sada zumunta na Facebook ya sanar da cewar wasu rukunin kamfanoni na Telecom na China wadanda suka hada da Huawei sun yi masa kutse don tatsar wasu bayanai na ma'abuta shafin. Wannan shi ne karo na biyu ke'nan da Facebook ke samun kansa cikin irin wannan hali bayan abin kunyar da ya faru na wani kamfanin Cambridge na Birtaniya watau Analytica wanda ake zargi da tattara bayyanai na ma'abuta shafin na facebook kusan dubU 87 don jirgita ra'ayoyinsu.