Trump zai dawo amfani da Facebook
January 26, 2023Kamfanin Meta ya sanar da shirin dage wa tsohon Shugaban Amirka Donald Trump takunkumin hana amfani da Facebook da Instagram, bayan kamfanin ya haramta masa shiga shafukan na tsawon shekaru saboda zarginsa ingiza magoya bayansa kai hari a majalisar dokokin kasar a watan Janairun 2021.
"Za mu dawo da shafin Mr. Trump na Facebook da Instagram a cikin makonni masu zuwa," in ji Nick Clegg, shugaban kamfanin Meta na harkokin duniya a cikin wata sanarwa. Ya kara da cewa matakin zai zo da "sabbin tsare-tsare don dakile sake aikata laifuka."
Tun bayan haramta masa amfani da shafukan a 2021, Mr Trumpo ya koma amfani da shafin sada zumunta mallakinsa da ya kaddamar mai suna Truth Social bayan da twitter suka dakatar da shi daga shiga shafin.
Ba a bayyana lokacin ko ranar da Trump zai fara amfani da dandamalin shafukan sada zumuntar ba, kuma makusantansa ba su yi martani kan neman karin bayani kan batun ba.
Amma Attajirin Mr. Trump mai shekaru 76 a duniya, ya mayar da martani ta hanyar da aka saba, yana mai cewa Facebook ya yi asarar biliyoyin daloli tun bayan dakatar da shi. "Kada irin wannan abu ya sake faruwa ga shugaban kasa mai ci, ko kuma wani wanda bai cancanci azaba ba!" Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Socia.
Facebook ya dakatar da Trump kwana guda bayan zanga-zangar ranar 6 ga Janairun 2021, lokacin da wasu gungun magoya bayansa da ke neman dakatar da shaidar shan kaye a zaben da ya yi da Shugaba Joe Biden, suka mamaye babban birnin Amirka da ke Washington.
Tsohon shugaban na Amirka kuma tauraron gidan talabijin, ya shafe tsawon lokaci yana yada cewa an sace masa nasararsa a zaben shugaban kasa kuma daga baya aka tsige shi saboda tada tarzoma.