Yan tawaye sun hana zaman lafiya a Goma
March 4, 2023A gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, 'yan tawayen M23 na kokarin tunkarar Goma. Garin Mushaki, wanda ke da nisan kasa da kilomita talatin daga Goma, ya fada hannunsu, kafin sojojin Kwango su karbeshi. Amma ana ci gaba da gwabza fada da mayakan M23 a kan tsaunukan wannan yanki mai tuddai. Yanzu haka ana aza ayar tambaya a game da inda 'yan tawayen ke samun kudaden sayen makamai har suka sha karfin dakarun gwamnatin.
Da farko dai yankunan da ke karkashin ikon kungiyar masu dauke da makamai na da tarin arzikin ma'adinai, bugu da kari, karbar haraji ba bisa ka'ida ba daga jama'a, al'ada ce da kungiyoyin 'yan tawaye suke yi domin samun kudaden shiga
Kwararru masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya a kan kasar, sun bayyana alal misali, a cikin wani rahoto da aka gabatar a watan Disamba na 2022 ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewar, harajin da Kungiyar M23 ta karba daga jama'a a kan iyakokin Bunagana da Kitagoma ya taimaka wajen samar da kudaden ayyukan kungiyar. Hakazalika a cewar Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar na karbar kusan dala dubu 27,000 a kowane wata a kan iyakar ta Bunagana kadai.
Kungiyar ta M23 na yin shelar cewa 'yan gudun hijira 'yan kabilar Tutsi 'yan asilin Ruwanda da ke zaune a arewacin Kwagon, suma suna taimaka mata. Akwai dimbin al'ummar Tutsi na Kwango da ke zaune a Ruwanda, mutanen da suka dade suna can kuma ba za su iya komawa gidajensu ba a Kwango. Sojojin Kwango na zargin Ruwanda da jibge sojoji a gabashin Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Kwangon 356 domin karfafa 'yan tawayen M23 abin da ya sa dangantaka tsakanin kasahen biyu ta yi tsami.