Siriya: Babu alamar tsagaita wuta
October 20, 2019Talla
Ma'aikatar harkokin tsaron kasar Turkiyya ce ta sanar da mutuwar sojanta guda a wani hari da mayakan 'yan tawayen Kurdawa suka kai kansu a kasar Siriya. Sanarwar ta kara da cewa, an budewa rundunarta wuta ba tare da mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da bangarorin biyu masu fada da juna suka cimma ba.
A ranar Alhamis da ta gabata ne, gwamnatin Turkiyyan ta amince ta dakatar da farmakinta a arewacin Siriya na kwanaki biyar don bai wa mayakan Kurdawa damar janyewa da kuma samar da wani sansani da za a tsugunar da 'yan gudun hijirar Siriya sama da miliyan uku da suka tsallaka Turkiyya.