1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faduwar jirgi a Lagos na Najeriya

June 3, 2012

Fasinjoji 153 da ke cikin jirgin Dana Air da ya taso daga Abuja sun rasa rayukansu a Lagos na kudancin Najeriya. Ba a bayyana musababbin faduwar jirgin ba.

https://p.dw.com/p/157J1
Bei einem Flugzeugunglück in Taiwan sind 79 Menschen ums Leben gekommen. Die Boeing 747 der Singapore Airlines stürzte bei schlechtem Wetter direkt nach dem Start in Taipeh ab.
Hoto: AP

A Najeriya wani jirgin sama da ke dauke da fasinjoji 153 ya fadi a birnin Lagos ba tare da an yi nasarar tsamo ko da mutun guda ba. Shugaban hukumar da kula da zirga zirgar jiragen sama na Najeriya Harold Denerun ya ce baya jin cewa akwai wani fasinja da ya tsira da ransa. wannan jirgi kirar MD 83 mallakar Dana Air da ya taso daga Abuja, ya fadi ne a kusa akan wasu gidaje da ke kusa da ke kusa da filin jirgin Lagos.

Tuni dai hukumomin Najeriya suka rufe filin tashi da kuma saukan jirage na Murtala Muhammed da ke lagos bisa dalilai na tsaro. Sai dai kuma wani jami'i da bai son a bayyana sunansa ba, ya ce an yi jinkiri wajen kai ma jirgin agajin da ya ke bukata. Da ma dai matukin jirgin ya sanar cewa ya na fiskantar matsala.

Wannan ya zo ne kwana guda bayan da wani jirgin kaya mallakar Alliesd Arir na Najeriya ya fadi a Accra na Ghana. A wannan Lahadin ne hukumomin ƙasar ta Ghana suka ƙaddamar da bincike domin gano musabbabin hatsarin, wanda yayi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 10. Rahotanni farko farko dai na nuni da yiwuwar tsinkewar birkin jirgin ne, yayin da rashin yanayi mai kyau kuma ya tsananta halin.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: zainab Mohammed Abubakar