1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma ya kai ziyarar tarihi Kanada

Ramatu Garba Baba
July 25, 2022

Fafaroma Francis ya nemi gafara daga iyalan daliban da aka kashe ko aka ci zarafinsu a wasu makarantun kwana da ke karkashin kulawar cocin Katolika a kasar Kanada.

https://p.dw.com/p/4EdE2
Kanada Edmonton | Besuch Papst Franziskus | Bitte um Entschuldigung, kirchliche Gewalt gegenüber Kindern
Hoto: Eric Gay/AP Photo/picture alliance

Shugaban darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya isa kasar Kanada cike da alhini a kokarin da yake na ganin an rage radadin ta'asar da limaman cocin Katolika suka aikata kan wasu 'yan asalin kasar Kanada da ake ganin tsiraru ne, da suka tsira daga nau'ukan cin zarafi a makarantun kwana na cocin Katolika. 

Da farko ya kai ziyara kaburan da aka binne mamatan inda ya gudanar da addu'o'i kafin ya gana da 'yan uwa da dalibai kusan dubu goma sha biyar da suka tsira daga ta'asar wancan lokacin, a yanayi na tausayawa ya nemi gafararsu. A bara aka soma bankado labarin gano gawarwakin daruruwan yara 'yan asalin kasar a cikin kaburbura da ba a bayyana ba, a makarantun gwamnatin da ke karkashin kulawar cocin katolikan, lamarin da ya janyo ma mahukuntan na Kanada suka daga sassan duniya.

Wannan na daga cikin matakan da Fafaroman ke dauka na magance badakalar cin zarafin kananan yara da ake zargin limaman cocin da yi amma aka shafe shekaru ana boyewa. Zai kwashi akalla kawanaki shida a ziyarar da za ta kai shi yankunan Alberta da Quebec da kuma wani yanki da ke arewacin kasar ta Kanada.