1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Fafaroma ya yi tir da kisan faren hula a Gabashin Kwango

June 16, 2024

Fafaroma Francis ya yi tir da Allah-waddai da rikicin da ake gwabzawa a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango tsakanin sojojin gwamnati da kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai inda ake zubar da jinin fararen hula.

https://p.dw.com/p/4h6es
Fafaroma ya yi tir da rikicin Gabashin Kwango
Fafaroma ya yi tir da rikicin Gabashin KwangoHoto: Alessandra Tarantino/AP/dpa/picture alliance

Babban Limanin na cocin Kotolika ya ce suna samun labarai masu bakanta rai a gamme da yadda ake kisan kare dangi wa fararen fula galibi mabiya addinin Krista a wannan yankin na Kwango, inda rikici ke daukar sabon salo a baya-bayan nan.

Karin bayani: Kungiyar IS ta kaddamar da hare-haren ta'addanci a Kwango

Kazalika Fafaroma Francis ya yi kira da babbar ga gwamnatin Kwango da kuma masu fada a ji a duniya da su yi duk mai yuwa don kawo kawo karshen wannan tashin hankali tare kuma da kare fararen hula da ba su ji ba su gani ba.

Karin bayani: 'Yan tawayen Kwango sun kashe fararen hula da dama

Kawo yanzu dai sama da mutane 150 rikicin na gabashin Kwango ya ritsa da rayukansu cikin har da mutum 42 da aka halaka a daren Laraba wayewar Alhamis din da ta gabata, lamarin da kungiyoyin fararen hula ke dora alhaki ga kungiyoyin 'yan ta'adda na AFD da kuma IS.