Fafutikar Afirka a yaki da sauyin yanayi
Nahiyar Afirka za ta fi ko'ina fuskantar barazanar sauyin yanayi. A saboda haka ne gwamnatoci da kungiyoyi da ma dai-daikun jama'a suka tashi tsaye domin bullo da dabarun magance matsalar.
Fafutikar Afirka a yaki da sauyin yanayi
Galibi dai kasashe masu karfin masana'antu ne ke da alhakin fitar da sinadarin Carbon CO2 da ke yi wa muhalli lahani. Sai dai kuma wadanda ke fama da radadin su ne kasashen kudancin duniya. A kasashen Afirka kuwa da suke fama da matsaloli kamar su fari da zaizayewar kasa da ambaliyar ruwa da kuma kwararowar hamada, mazauna nahiyar sun fara tsara dabarun magance matsalar.
Mutane da dama sauyin yanayi zai iya rabawa da muhalli a Afirka
Kasar Muzambik ce kasar da ta fi matsaloli masu nasaba da yanayi. Dukkanin wuraren da ke gabar ruwan garin Beira sun soma ganin tsananin bala'in ambaliya. Kwararru sun ce barnar da ambaliyar ke yi ta ninka ta yake-yake ta fuskacin raba mutane da muhallinsu. Hasashe ya nunar da cewa nan da shekaru 10 masu zuwa, kimanin mutane miliyan 20 ne matsalar sauyin yanayin za ta raba da muhallinsu.
Kanda garki daga yawan ruwa da zai zo daga Teku
Hukumar da ke nazarin matsalolin sauyin yanayi IPCC, ta yi kiyasin cewa ruwan teku zai karu da maki 40 zuwa 80 nan da shekara ta 2100. Don haka ne ma Muzambik ke daukar matakan fadada hanyoyin ruwa a Kogin Beira daga tsakiya da kuma kara kaimi wajen shuka bishiyoyi. Haka nan kasar tana gina wasu gine-gine masu tsawo da za su iya samar da kariya.
Matakan shuka bishiyoyi a Afirka
A nan rairayin hamada ne ke dosar wasu daga cikin gonaki a kudancin saharar Afirka. Kasashe 11 ne ke kokarin shawo kan wannan matsalar a wani yanki mai nisan kilo 7,750 ta hanyar shuka bishiyoyi. Saiwoyin bishiyoyin suna inganta yanayin kasa domin kasar na samun dausayi mai kyau da ke kore hamada. Sai kuma abincin da mutane dama dabbobi ke samu domin rayuwa.
Matakan hana zaizayewar kasa
Matsalar zaizayar kasa dai wata babbar barazana ce ga rayuwar manoma a sassan Afirka da dama. Ta hanyar amfani da tsarin noman rani na musamman, manomi irin Sounna Moussa a Nijar na dawo da albarkar kasar noma. Wannan dabarar dai ta iyaye da kakanni ce wadda kusan a iya cewa tana shudewa. Masana na bayar da shawarar noma nau'ikan abincin gargajiya da suka fi dace wa da kasa.
Ta'adin makamashin wutar lantarki na Dam
Wutar lantarki da ake samu daga ruwa na zaman kan gaba a duniya a nau'in makamashi da ake sabunta wa. A takaice an fi amince wa da tsarin saboda inganci da kuma rashin yin illa ga muhalli. Sai dai a yanzu kungiyoyi da sauran jama'a na bijire masa saboda a wasu lokutan ana sare daji mai fadin gaske ko ma tashin wasu ko wani kauye baki daya, a kokarin gina Dam da nufin samar da wutar lantarkin.
Makamashi mara gurbata muhalli a Afirka
Dukkanin kasashen Afirka za su wadatu da wutar lantarki a shekara ta 2030. Wannan matsayi ne da shugabannin kasashen nahiyar suka cimma yayin taron sauyin yanayi da aka yi a birnin Paris a shekara ta 2015. An shirya samar da wuta marar lahani ga muhalli mai karfin gigawatt 300 a kowace shekara. Daya daga cikin dabarun shi ne samar da makamashi mai amfani da iska wanda aka soma a kasar Habasha.
Matakan samar wa kai hasken wutar lamtarki
Yanzu mutane da dama a Afirka sun koma nema wa kansu hanyoyin samun wutar lantarki ba tare da dogaro da injina masu aman hayaki ko kuma ta gwamnati mara tabbas ba. Saukin farashin na'urar wuta mai amfani da hasken rana ya sanya samun wutar cikin sauki. Ga misali ana iya gani a asibitoci ko makarantu kai har ma da gidaje akwai irin wadannan fitilu masu amfani da hasken rana.
Amfani da robobi wajen gini
A nahiyar Afirka a yanzu batun sake sarrafa kayayyaki da yin amfani da su ta wasu hanyoyi ya mamaye ko'ina. A Najeriya mutane suna gina gidaje ta hanyar amfani da robobin ruwan sha ko kuma lemo da a baya suke zama barazana ga muhalli. Alkaluma sun yi nuni da cewa akalla robobin ruwa da aka yi amfani da su miliyan guda ne ake sayensu a kowane minti guda a fadin duniya domin sake aiki da su.
Wata 'yar fafutikar kare muhalli a Tanzaniya
Getrude Clement ta himmatu ga aikin kare muhalli. A kowane mako 'yar kasar ta Tanzaniya wacce bata cika shekarun balaga ba, na fadakar da mutane ta Rediyo irin matakan da suka dace a rika dauka domin kare muhalli. A cewarta hakan zai taimaka wajen samar da ruwa mai tsafta. A nan tana jawabi ne a gaban zauren taron Majalisar Dinkin duniya a birnin New York na Amirka cikin watan Afrilun 2016.
Nahiyar Afirka na bukatar kwararrun masana yanayi
Yadda nahiyar Afirka za ta iya jure wa sauyin yanayi zai dogara ne da yadda al'ummomi daga kananan hukumomi zuwa ga shiyoyi suka fahimci illolin gurbata muhallin. Don haka ne kungiyar masu nazarin kimiyya ta kudancin Afirka SASSCAL ke kokarin fahimtar da al'umma, inda take samun tallafi daga Jamus. Burin kungiyar shi ne: rage illar sauyin yanayi a kan harkokin noma da kuma ruwa.