Fafutikar marigayi Kofi Annan
Dan asalin Ghana, Kofi Annan ya kasance bakar fata na farko da ya rike mukamin Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, inda ya taka rawa wajen wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya da dama.
Tauraro a Majalisar Dinkin Duniya
An haifi Annan ne a shekarar 1938 a kasar Ghana, kuma ya yi karatunsa a kasashen Swizaland da kuma Amirka. Ya soma aiki da Majalisar Dinkin Duniya yana dan shekaru 24 da haihuwa. A shekarar 1993, aka ba shi mukamin shugaban sashen wanzar da zaman lafiya. Kalubalen da ya soma fuskanta shi ne, warware rikicin kasar Somaliya, inda aka samu asarar rayuka na sojojin Amirka 18 a yayin wani gumurzu.
Rashin nasara a Bosniya da Ruwanda
Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta gaza shawo kan rigingimu da suka kai ga haddasa kisan kiyashi a Bosniya da Ruwanda a shekarar 1990. Wannan ya zaburar da Kofi Annan kan sanin makamar aiki da kuma matakin da ya dace a dauka don kauce wa rikici da ya keta haddin dan Adam, kamar yadda ya rubuta a wani littafi na tarihin rayuwarsa da aka wallafa a shekarar 2012.
Goyon bayan Amurka
A shekarar 1996, Amirka ta shirya tsige sakataren Majalisar Dinkin Duniya na wancan lokaci, Boutros Boutros-Ghali, a sanadiyar sabani a tsakaninsa da mahukuntan na birnin Washington. Daga bisani Amirka ta yi nasarar fidda Boutros-Ghali duk da yunkurinsa na son yin tazarce, lamarin da ya bai wa Annan damar dare kujerar a shekarar 1997.
Kyautar lambar yabo ta zaman lafiya
A shekarar 2001, kwamitin kyautar yabo na Nobel, ya karrama Majalisar Dinkin Duniya da sakatarenta Kofi Annan, an yabe shi da farfado da muradun majalisar da kuma 'yancin dan Adam. A jawabinsa a yayin karbar kyautar, ya ce ''kyautar ta kowa ce'' ya kuma gode wa kwamitin a madadin sauran abokan aikinsa, musanman wadanda suka jefa rayuwarsu cikin hadari a kokarin samar da zaman lafiya.
Sabani da fadar Washington
Amirka ta kai mamaya a Iraki a shekarar 2003, bayan da ta yi watsi da shawarar Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da sauran abokan kawancenta kan guje wa farmakin. Annan ya fito karara inda ya soki matakin da ya ce, abu ne da ya karya dokar kasa da kasa, kalaman da suka fusata mahukuntan na Washington da suka dade suna mara masa baya.
Bincike
Mr. Annan ya sami kansa cikin badakalar rashawa, kan wani tsari na kudin musayar mai da abinci na kasar Iraki a shekarar 2004, an ambato dansa Kojo da laifin karbar kudi daga kamfani mai alaka da tsarin. Daga karshe an wanke sakataren daga duk wani zargi na aikata ba daidai ba, sai dai an ci gaba da aza ayar tambaya kan gaskiyar zance a bangaren Kojo. An danganta zargin da bita-da-kullin Amirka.
Fafutuka bayan ajiye aikin Majalisa
Annan ya kammala wa'adinsa na shekaru 5 a shekarar 2006, inda Ban Ki-moon ya gaji kujerar, sai dai dan asalin kasar Ghana ya ci gaba da taka muhinmiyar rawa a lamuran duniya. Tare da Nelson Mandela, da Desmond Tutu, da wasu shahararrun mutane, ya samar da kungiya mai zaman kanta mai suna ''The Elders'' a fafutukarsa ta samar da zaman lafiya da kuma 'yancin dan Adam.
Gazawar samar da zaman lafiya a Siriya
An ci gaba da ganin Annan a bainar jama'a, bayan da ya karbi aikin wakilcin tawagar Majalisar Dinkin Duniya zuwa Siriya a shekarar 2012, a rikicin da ya rikide zuwa yakin basasa. Sai dai daga bisani ya yi murabus daga wannan mukamin bayan watanni biyar. Dalilinsa shi ne yadda manyan kasashen duniya suka yi biris kan magance rikicin, ya ce ''na rasa sojoji a kan hanyarsu ta zuwa birnin Damascus''
Aikinsa na karshe a Myanmar
A shekarar 2016, Annan ya wakilici wani kwamitin wanzar da zaman lafiya zuwa Myanmar, mabiya addinin Buddha masu rinjaye sun yi boren nuna adawa. Daga bisani kwamitin ya shawarci gwamnati da ta yaki talauci ta bai wa al'ummar Rohingya 'yancinsu. A watan Oktobar 2017, Annan ya matsa wa Majalisar Dinkin Duniya kan daukar matakin mayar da 'yan Rohingya da suka tserewa rikici gidajensu.