220310 Palästinenser Siedlungen
March 23, 2010A halin yanzu haka gwamnatin Piraminista Benjamin Natanyahu tana shan kakkausan suka sakamakon shirinta na gina sabbin gidajen Yahudawa a gabacin Ƙudus.
Kimanin Yahudawa 'yan share wuri zauna dubu ɗari biyar ne ke kaka-gida a yankunan Palasɗinawa a yammacin gaɓar kogin Jordan da gabacin Ƙudus. Kuma idan da so samu ne da gwamnatin Isra'ila zata fi ƙaunar ganin sun ci gaba da zama a can har sai illah masha'a Allahu. Domin kuwa Isra'ilar na fatan tabbatar da manyan matsugunan a hannunta a duk wata yarjejeniya ta zaman lafiyar da za a cimma. A sakamakon matsin lamba daga Amirka Piraministan Isra'ilar Benjamin Natanyahu ya dakatar da gine-ginen tsawon watanni goma a cikin watan nuwamban da ya wuce, in banda a gabacin Ƙudus, saboda Isra'ila na iƙirarin mallakar dukkan birnin kuma tana bakin ƙoƙarinta wajen hana mayar da gabacin Ƙudus fadar mulkin wata ƙasa ta Palasɗinu da za a kafa nan gaba. Tun ma kafin tashinsa zuwa Amirka a baya-bayan nan sai da Piraminista Natanyahu ya bayyana cewar Isra'ila har kwanan gobe zata ci gaba da gina matsugunan Yahudawa a gabacin Ƙudus:
"Babu wani banbanci tsakanin manufofinmu da na sauran gwamnatocin Isra'ila da suka gabata a cikin shekaru 42 da suka wuce. A ganinmu gine-gine a birnin Ƙudus daidai yake da gine-gine a Tel-Aviv."
A yankin gabacin Ƙudus ana ci gaba da ƙuntata wa Palasɗinawa da cin zarafinsu, kamar yadda wata Bajamushiya malamar kimiyya Helga Baumgarten dake koyarwa a jami'ar Bi'rZeit dake Ramallah take kuma zaune a gabacin Ƙudus ta nunar.
"Wata sabuwar manufar da aka fuskanta a yanzu ita ce ta kakkaɓe Palasɗinawa daga wani yanki na birnin baki ɗaya. Hakan na ma'ana ne cewar mun shiga wani mummunan hali na zaman ɗarɗar a birnin Ƙudus. Abin dai dake faruwa a yanzu wani yunƙuri ne na tabbatar da birnin Ƙudus a matsayin fadar mulkin ƙasar ta Yahudawa. A ƙarƙashin wannan manufa Palasɗinawa, waɗanda mazauna Ƙudus ne, ba su da ikon zama a birnin."
A nasu ɓangaren Palasɗinawan na tattare da takaici game da ci gaba da giggina matsugunan na Yahudawa da ake yi. A halin yanzu haka an karkasa yankin gaɓar yammacin kogin Jordan ta yadda da wuya a iya gina wata sahihiyar ƙasa da zata wanzu kafaɗa-da-kafaɗa da Isra'ila, in ji Nur Masalha, Bafalaɗine kuma masani akan kimiyyar siyasa.
"Ta yaya za a iya kafa wata ƙasa ta Palasɗinawa, wadda aka karkasa ta akan kashin biyar cikin ɗari na harabarta. Isra'ilawa a taƙaice sun yi wa manufar wanzuwar ƙasashe biyu kafaɗa-da-kafaɗa da juna zagon ƙasa."
Hatta a fadar mulki ta Berlin an bayyana damuwa game da halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya da kuma makomar shawarwarin zaman lafiyar yankin. A makon da ya wuce sai da shugabar gwamnati Angela Merkel ta fito fili tana sukan manufar giggina matsugunan da kakkausan harshe lokacin ganawarsu da Piraministan Lebanon Sa'ad Hariri.
Mawallafi: Ahmad tijani Lawal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi