Fafutukar yaki da cin hanci a Nijar
April 20, 2022Duk da cewa akwai mutane da dama da yanzu haka suke tsare dangane da batutuwa na sama da fadi da dukiyar kasa, amma a wannan karo kotun da ke kula da shari'ar da ta shafi almundahana da dukiyar kasa, ta yi babban kamu, inda bayan da ya gurfana a gabanta, ministan sadarwa na kasar ta Nijar Mahamdou Zada ya tsinci kanshi a gidan kaso na garin Kollo da ke da nisan yar tazara da Yamai babban birnin kasar ta Nijar. Ko ma da yake abubuwan da ake tuhumar shi da su ba wai ya yi sune yana a matsayin minista ba, amma kasancewar yana minista mai ci aka kamashi lamarin ya haifar da ra'ayoyi mabambanta a kasar ta Nijar. Alhaji Idi Abdou, tsohon jami'in yaki da cin hanci da karbar rashawa a Jamhuriyar Nijar ya ce ya kyautu a jinjina wa mashara‘anta da ma shugaban kasar ta Nijar.