Kogin Nilu: Kokarin sasanta rikici
June 27, 2020Talla
Wata sanarwa da suka fitar a baya-bayan nan, na zaman babban mataki wanda ka iya yayyafa ruwa a kan wutar da ta kunno kai tsakanin kasashen uku.
Rigama a kan Kogin na Nilu wanda ya ratsa kasashen uku, ta fara ruruwa tun kusan shekaru 10 da suka wuce. Sai dai yunkurin Habasha na datse wani bangare na kogin don aiwatar da shirinta na samar da hasken wutar lantarki ga kasarta ya samu turjiya, inda Sudan da Masar suka nuna cewa ta wannan kogi ne suke samun ruwan sha.
Kasashen Sudan da Masar din dai sun bayyana cimma wata yarjejeniya a ranar Jumma'ar da ta gabata, biyo bayan wani taro da suka yi a karkashin kungiyar Tarayyar Afirka AU, da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya jagoranta.