Falasdinawa a Gaza na cikin mawuyacin hali
Adadin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a Gaza na karuwa yayin da Isra'ila ke ci gaba da daukar fansa na hare-haren ta'addancin Hamas.
Isra'ila ta tsananta hare-haren ramuwar gayya a Gaza
Isra'ila ta tsananta kai hare-hare ta sama a zirin Gaza kwanaki bayan da Hamas ta kaddamar da hare-hare. Kungiyar EU da Amurka da sauran kasashe sun ayyana Hamas mai iko da Gaza a matsayin kungiyar ta'addanci. Firayiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce "abin da za mu yi wa makiyanmu a cikin kwanaki masu zuwa za a jima ba a manta ba."
An lalata gine-gine masu yawa
Daruruwan gine-gine ne suka lalace gaba daya, daura da wasu dubbai da suka lalace sosai sakamakon hare-haren Isra'ila, a cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA). Dubban mutane ne aka ce ba su da ruwa.
Neman wadanda suka makale
Masu aikin ceto na neman wadanda suka tsira bayan harin da Isra'ila ta kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza. Ya zuwa yanzu, sama da mutane 1,000 suka mutu yayin da wasu fiye da 5,000 suka jikkata bayan hare-haren jiragen sama a yankin da ke karkashin ikon Hamas, a cewar hukumomin yankin.
Makokin wadanda suka mutu
Wata mata ta yi kuka yayin da aka dora gawarwaki a kan babbar mota, bayan wani harin da Isra'ila ta kai. A cewar hukumar lafiya ta Gaza, an kashe fiye da yara 200 da mata sama da 100 a Gaza.
An rufe Gaza
Falasdinawa na tserewa harin Isra'ila. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, fiye da mutane 187,000 ne a Gaza suka rasa matsugunansu, kana sama da dubu 100 suka yi mafaka a makarantun MDD, yayin da wasu 40,000 suka kaurace wa gidajensu. Shi kansa ficewa daga zirin Gaza abu ne mai wuya kasancewar Isra'ila ta rufe yankin tare da rufe mashigar Masar.
Sojojin Isra'ila suna iko da iyakar Gaza
Ana ganin sojojin Isra'ila suna sintiri a kan iyakar Isra'ila da Gaza. Mayakan Hamas sun kutsa shingen kan iyaka a wurare da dama a cikin daren ranar 7 ga watan Oktoba kafin su kai hare-hare a yankin Isra'ila. Isra'ila ta gina shinge kan iyakar Gaza a shekara ta 1994. An kuma rufe kan iyakar Gaza da Masar da dogon shinge.
Sojojin Isra'ila su na kan iyakar Gaza
Bayan da Isra'ila ta fitar da karin sojoji 300,000, mazauna Gaza da dama na fargabar cewa, akwai yiwuwar kaddamar da harin Isra'ila ta kasa. Motocin soji da kayan yaki sun cika kan iyakar Gaza. An kwashe kusan dukkan mautanen da ke garuruwan Isra'ila da ke kan iyaka da Gaza gaba daya.
Mummunan yanayi na bukatar jinkai
Da yake magana da CNN, Jan Egeland, babban sakataren hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Norway, ya yi gargadin tagaiyarar al'umma a Gaza. "Zai kai ga aikata laifukan yaki idan yara za su mutu da yunwa a asibitoci saboda rashin wutar lantarki misali,"
Shugaban Hamas a Gaza, Yahya Sinwar
Yahya Sinwar ya kasance shugaban kungiyar Hamas a Gaza tun a shekarar 2017. Ana masa kallon daya daga cikin wadanda suka shirya harin ta'addancin da aka kai kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba. An ambato Sinwar, wanda ya taso a sansanin 'yan gudun hijira na Gaza yana cewa, "gwamma mu mutu a matsayin shahidai da mu mutu saboda zalunci da wulakanci."
Tsanantar tashe-tashen hankula
Wani mai magana da yawun Hamas ya shaida wa manema labarai cewa, a duk lokacin da Isra'ila ta kai hari a kan fararen hula a Gaza ba tare da yin gargadi ba, to za a kashe daya daga cikin 'yan Isra'ila da ake garkuwa da su. Ministan harkokin wajen Isra'ila Eli Cohen ya yi gargadin cewa babu yafiya kan irin wannan mataki.