1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Taron tsaro na birnin Munich

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 17, 2023

Minstan tsaron Jamus Boris Pistorius ya jadda bukatar samar da karin Euro biliyan guda, domin inganta fannin tsaron kasar.

https://p.dw.com/p/4NesD
Jamus | Munich | Taron Tsaro na Duniya | Boris Pistorius
Ministan tsaron Jamus Boris PistoriusHoto: DW

Minstan tsaron na Jamus Boris Pistorius ya bayyana hakan ne gabanin bude taron tsaro na shekara-shekara a birnin Munich na kasar, inda shugabannin kasashe da jiga-jigan al'umma ke halarta ciki har da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da kuma Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine. Yakin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine na cikin abin da ya dauki hankalin taron, wanda yake zuwa kimani shekara guda bayan Rasha ta kaddamar da kutse a makwabciyar tata.