'Fannoni a Namibiya' - hotunan bayan mulkin mallaka
Shekaru 25 bayan 'yancin kai, shin yaya Namibiya take bayan mulkin mallaka? Ma'aikata da wadanda ba sa aiki da dalibai da kuma manoma na daga cikin mutanen da suka dauki hotunan rayuwarsu ta yau da kullum.
Abin daukar hoto ga kowa da kowa
A shekarar 2007 wasu Jamusawa biyu, Evelyn Annuss 'yar kimiyyar wasan kwaikwayo da 'yar fasaha Barbara Loreck, sun rarraba kyamarori ga daruruwan 'yan Namibiya a matsayin wani aikin gwaji. Sun bukacesu su dauki hotunan yadda kasarsu take yanzu shekaru 25 bayan 'yancin kai, shekaru 25 bayan zamanin mulkin mallakan Jamusawa da 'yancin kai. Paulus Jacobs mazaunin Lüderitz ya dauki wannan hoton.
Jamusawa na da na su shirin, 'yan Namibiya kuma na da na su
"Babban burinmu shi ne mu ga hotunan tunanin mutane game da 'Germanness' a Namibiya," inji Annuss a cikin wata hira da DW. "Amma sakamakon ya kasance wani abu daban. Mutane ba su nuna wata sha'awa ga tarihin mulkin mallaka ba. Maimakon haka sun mayar da hankali a kan rayuwarsu ta yau da kullum a gaban kyamarorin." Clemensia Haragaes ta dauki hotunan unguwar Katutura da ke birnin Windhoek.
Kyamara a nan, kyamara a can
An dauki hotuna fiye da 5,000 lokacin da aka yi balaguro da kyamarorin a fadin kasar Namibiya. An bukaci masu daukar hoton su rubuta sunayensu a kan kyamarorin. Amma 'yan Namibiyar ba su ba wa hakan muhimmanci ba. "Mun yi kokarin gane wadanda suka dauki hotunan, amma hakan bai yiwu ba domin mutane ba su yi sha'awar haka ba." Annuss na ganin wannan a matsayin wani kyakkyawan sakamakon aikin fasaha.
Daga Windhoek zuwa Switzerland
A dangane da bikin cika shekaru 25 da samun 'yancin kan Namibiya a ranar 21 ga watan Maris, gidan tarihin Afirka a birnin Basel da ofishin jakadancin Namibiya a Switzerland sun baje kolin hotuna a Basel da Geneva. A shekarar 2009 gidan tarihin kasa a birnin Windhoek ya baje koli mai taken "Staging made in Namibia." Wannan hoton da Memory Biwa ya dauka na daga cikin hotunan da aka nuna.
Kawata hotunan yau da kullum
Gaba daya hotunan na yau da kullum da akasari aka dauka nan-take, sun dauki hankalin masu fasaha: An yi musu gangar jiki an rataya a gidan tarihi da fasaha na kasa a Namibiya. "Ya kasance muhimmi ga masu daukar hoton su ga aikinsu a can, domin daukacinsu sun fito ne daga tsoffin unguwannin wajen gari na talakawa." Marama Kavita daga Okakarara,Otjozondjupa ta dauki wannan hoton.
Wasan kwaikwayo na yau da kullum
Akasari hotunan sun yi tuni da hotunan wasan kwaikwayo da fina-finai. "Mutane sun yi shiga iri daban-daban kuma sun yi wasan kwaikwayo daban-daban a gaban kyamara," inji Evelyn Annuss. Wadannan hotuna sun banbanta da sauran hotunan da a kan dauka don nuna wasu sigogi na musamman, musamman hotunan Namibiya da aka fi ganinsu a Jamus. Mai daukar hoto: Anke Langmaak: bikin Carnival a Windhoek.
Rayuwata ta yau da kullum
Wani gungun mata 'yan Herero a gaban wasu tantuna, wata yarinya ta yi shiga irin ta 'yan yawon bude ido tana tsaye a gaban hoton wata barewa sannan kananan yara na bikin carnival a birnin Windhoek; hotuna daban-daban na rayuwar yau da kullum daga bangarori mabanbanta. An kira hoton da Marama Kavita ta dauka 'Herero Day in Okahandja.'
Na nuna maka yadda kake gani na
Lokuta masu ban al'ajabi. Masu daukar hoton sun dakushe tunanin yadda muke kallon rayuwa a Namibiya, inji Evelyn Annuss. Ana iya takaita sakamakon kamar haka: "Na nuna maka yadda kake gani na," kamar yadda wannan hoto da Cesilie Benjamin ta dauka ya nunar. An tattara hotuna da aka baje kolin a Basel da Geneva a cikin wani kundi. Mai daukar hoto: Cesilie Benjamin, Otjiwarongo.