Jamus na duba yiwuwar dawo da wasu matakan yaki da Corona
September 16, 2022Talla
Daga cikin sabbin dokokin da majalisar zartarwar Jamus ke shirin dubawa su fara aiki a farkon watan Oktoba na 2022 sun hada da tilasta saka takunkumin fuska a cikin jiragen kasa idan ana tafiya mai nisa da asibitoci, sai dai sauran jihohi na iya amfani da matakin don tilasta amfani da takunkumi a gidajen cin abinci, kana ana shirin dage amfani da dokar saka takunkumin fuska ga masu tafiye-tafuiye a jirgin sama.
Jamus ta kuma bayyana anniyarta na kin sake komawa a duk wasu matakan dokar kulle a wuraren kasuwanci da makarantu a cewar ma'aikatar kiwon lafiya ta kasa.