Kwarya-kwaryar yarjejeniya a Idlib
March 6, 2020Talla
Rahotanni daga yankin Idlib na kasar Siriya sun tabbatar da cewa yarjejeniyar da Turkiyya da Rasha suka cimma ta tsagaita buda wuta ta soma aiki a yau Jauma'a 06.03.2020 a wani yunkuri na dakatar da gumurzu takanin dakarun Siriya masu goyoyn bayan Rasha da na Turkiyya.
Kungiyar kare hakin bil'Adama mai sa ido kan harkoki a kasar ta Siriya ta tabbatar da soma aiki da kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wutar bangarorin suka cimma a yankin Idlib.
A yammacin jiya Alhamis ne dai shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan suka gana tare da bayyana matakin yin aiki tare don kaucewa fito na fito a Siriya inda daga bisani suka sanar da cimma yarjejeniyar a lardin na Idlib da ke arewa maso yammacin Siriya.