1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Farfado da tattalin arzikin Jamus bayan Coronavirus

Suleiman Babayo MNA
April 20, 2020

Gwamnatin Jamus ta fara bude harkokin tattalin arziki sannu a hankali bayan fara samun lafawar annobar cutar numfashi ta Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3bAZt
BG Deutschland Corona Lockerung
Hoto: Getty Images/L. Baron

An fara aiki da matakan gwamnatin Jamus na fara bude harkokin kasuwanci sannu a hankali inda aka fara da kananan shaguna, yayin da nan da makonni biyu za a kai ga sauran harkokin tattalin arzikin. Tuni Shugabar gwamnati Angela Merkel ta soki wadanda suka nemi rage matakan da aka bukaci masu shagunu aiwatarwa saboda kariya daga cutar Coronavirus.

Merkel ta nuna damuwa kar fitowar mutane da yawa lokaci guda ya kassara nasarar da aka samu na rage yaduwar cutar ta Coronavirus.

A daya bangaren kasar Spain da ke cikin kasashen Turai da wannan cuta ta fi shafi za ta samu koma-bayan tattalin arziki tsakanin kashi 6.6 zuwa 13 cikin 100 a wannan shekara ta 2020. Babban bakin kasar ta Spain ya bayyana haka a wannan Litinin cikin wata sanarwa da ya fitar.