1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai za ta mayar da 'yan gudun hijira

Zainab Mohammed AbubakarMarch 19, 2016

A wannan Lahadin ce za'a fara komar da 'yan gudun hijirar da ke tsibiran Girka, bisa tsarin yarjejeniyar da kungiyar Tarayyar Turai wato EU ta cimma da Turkiya.

https://p.dw.com/p/1IGQu
Daruruwan 'yan gudun hijira ne ke kokarin shiga Girka daga Turkiya
Daruruwan 'yan gudun hijira ne ke kokarin shiga Girka daga TurkiyaHoto: DW/D. Tosidis

Hukumomin kasar ta Girka sun nunar da cewa aiwatar da yarjejeniya da kungiyar Tarayyar Turai ta cimma da Turkiya zai dauki lokaci kasancewar akwai wasu muhimman batutuwa da har yanzu ba'a kai ga warware su ba. Batutuwan dai sun kunshi yadda za a tantance sababbin 'yan gudun da ke shiga Turkiya domin sake mayar da su inda suka fito. Firaministan Turkiya Alexis Tsipras ya gana da ministocin kasar da manyan jami'ai da ke da ruwa da tsaki a batun matsalar 'yan gudun hijirar. Ganawar dai na zuwa ne sao'i bayan cimma yarjejeniyar ta Brussels, na komar da 'yan gudun hijirar da ke tsibiran Girka zuwa Turkiya, wanda zai fara aiki daga wannan Lahadi 20 ga watan Mari da muke ciki. A cewar mataimakin ministan harkokin cikin gidan Girka Yiannis Balafas, fara tantance 'yan gudun hijirar da ke Tsibiran kasar kafin a mayar da su, aiki ne da ke bukatar karin jami'ai wadanda Turai din ta yi alkawarin samarwa. A yanzu haka dai Girka na sa ran samun kwararrun jami'ai kimanin 23,000 daga nahiyar Turai, wadanda suka hadar da jami'an shige da fice da masu tafinta domin taimakawa wajen aiwatar da yarjejeniyar.