Zanga-zangar adawa da dokar 'yan fansho a Faransa
December 17, 2019Talla
Yajin aikin na ci gaba da daidaita fannoni da dama na kasar musamman ma fannin sufurin jama'a da na kasuwanci a daidai lokacin da bukukuwan Kirismeti ke kara karatowa.
Tuni firaministan kasar ya gayyaci kungiyoyin 'yan kwadagon kasar zuwa wata tattaunawa a ranar Laraba, a yunkurin da hukumomin kasar suke ta yi na neman kawo masalaha tsakanin bangarori da dama da ke adawa da sabuwar dokar.