1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Salula don yakar cutar coronvirus a Faransa

Abdoulaye Mamane Amadou
May 28, 2020

Majalisun dokokin Faransa sun amince da wani sabon tsarin da zai amfani da wayoyin salula domin yaki da yaduwar annobar coronavirus a kasar.

https://p.dw.com/p/3csGu
Frankreich Paris | Coronavirus | App StopCovid
Hoto: Getty Images/AFP/T. Samson

Daukacin majalisun sun jefa kuri'ar na'am ne da sabon tsarin da zai ba da damar amfani da wata sabuwar manhaja mai suna StopCovid, da za ta kasance a wayoyyin salula na jama'a, inda hakan zai bai wa hukumomin kasar damar tatsar wasu muhimman bayyanai kan mutumin da ya kamu da cutar ko kuwa ma ya kusanci wani wanda ke dauke da annobar ta Covid-19 nan take a cikin dan takaitacen lokaci, kana kuma hakan zai bai wa mutumin damar zuwa binciken lafiyarsa.