1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattauna batutuwan tsaro tsakanin Faransa da G5 Sahel

Abdoulaye Mamane Amadou
June 30, 2020

Shuwagabannin kasashen G5 Sahel da na Faransa za su yi wani zama na musamman don tattauna inda aka kwana game da batun yaki da ta'addanci a yankin sahel a birnin Nouakchott na kasar Murtaniyya.

https://p.dw.com/p/3eXyn
Frankreich G5-Sahel Gipfel in Pau
Hoto: DW/F. Tiassou

Ganawar na zaman irinta ta farko ga shuwagabannin kasashen na Nijar Mali Burkina Faso Chadi da Murtaniyya za su yi tun bayan bullar annobar corona, kana kuma tana shirin duba batutunwan tsaro da yaki da aiyukan ta'addancin da ya daidaita kasashen biyar, musamman ma yunkurin kakkabe mayakan jihadi a tsakanin iyakokin Nijar da Burkina Faso da Mali inda masu da'awar jihadin suka yi kaka gida.

Rahotanni na nuni da cewar a baya bayan dai rundunar tsaro ta Barkhane hadin gwiwa da takwarorinta na kara matsa kaimi ga mayakan jihadin, duk da yake a share daya ana kokawa da yawan cin zarafin bil'adama musamman ma kisan fararen hula daga sojojin kasashen lamarin da ya kara ta'azzara yakin.