SiyasaGabas ta Tsakiya
Faransa da Jamus da Burtaniya na son a dakatar da yakin Gaza
August 12, 2024Talla
Kasashen na Turai dai sun nuna bukatar kasashen Amurka da Masar da ma Qatar, su daage wajen ganin an cimma tsagaita wuta, ta yadda za a sako wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su - da ma samun shigar da kayyakin jinkai a Zirin Gaza.
Sanarwar da ke da nasaba da wannan bukata dai, ta samu sa hannun Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da kuma Firaminista Kier Starmer na kasar Burtaniya.
Masu shiga tsakanin sun kwashe watanni suna kokarin bangarori masu yaki da juna sun amince da yarjejeniyar da za ta ba da damar samun daidaito a tsakani.
A ranar Alhamis da ke tafe ne dai ake sa ran komawa zaman tattaunawa domin ganin yadda za a cimma yiwurar dakatar da kai hare-hare a yankin falasdinu.