Faransa da Sahel sun hadu kan yaki da ta'adda
January 14, 2020Yayin ganawar da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi da shugabannin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da Moritaniya da kuma Chadi a birnin Pau ra anar Litinin, Faransar ta ce za ta kara yawan sojoji 220. Rundunar hadin gwiwar ta Barkhane bisa amincewar taron na jiya za ta ba da karfi ne iyakoki uku na kasashen tare da taimakon kasashen Turai.
Shugaba Macron ya ce manufofi biyu masu karfi suka sanya gaba, wadanda suka hada da na soji da na siyasa. Manufar sojin ita ce ta iyakoki uku. Abin da za su fifitawa shi ne yaki da mayakan IS a yankin Sahara, wanda kuma ba zai hana su kaddamar da yaki kan sauran kungiyoyi masu makamai ba.
Mr. Macron ya sami nasarar da yake bukata, musamman samun hadin kan kasashen dangane da ci gaba da kasancewar dakarun Faransa a yankin, abin kuma da al'umomin kasashen biyar ke suka.