Faransa ta fada cikin yanayi na jimami
April 16, 2019Talla
Da yammancin jiya Litinin gobara ta tashi a katafariyar majami'ar da ke a tsakiyar birnin Paris. Ba zato ba tsanmani jama'a suka soma ganin hayaki ya mamaye sararin samaniyar birnin, al'amarin da ya haifar da rudani.
A jawabin farko bayan aukuwar lamarin, kakakin majami'ar ya shaidawa manema labarai cewar gobarar ta janyo barna, inda aka rasa mahinman abubuwa na tarihi.
An danganta faruwar gobarar da wani aikin sabunta ginin da ke gudana a majami'ar mai shekaru akalla 850. Sai dai a cewar karamin ministan cikin gida Laurent Nunez, ba a kamalla binciken da zai tabbatar da musababin gobarar ba tukun na.