Faransa ta yi juyayin mutuwar Déby na Chadi
April 20, 2021Cikin sakon ta'aziyya da ta mika wa dangin Shugaba Déby da al'ummar Chadi baki daya, fadar mulki ta Paris ta ce kasar ta yi rashin gwarzon soja, kuma shugaba da ya yi aiki ba ji ba gani don tabbatar da tsaro da kuma zaman lafiya na tsawon shekaru talatin.
Amma kuma gwamnatin ta Faransa ta yi kira da a gudanar da tattaunawa da dukkan 'yan wasan siyasa da kungiyoyin farar hula, da zummar damawa da kowa da kowa a kokarin maida mulki a hannun zababbiyar gwamnati.
Sabuwar gwamnatin mulkin soji da Mahamat Deby Itno da ke zama da ga marigayi ke jagoranta, ta rusa majalisar gudanarwa ta gwamnati tare da dakatar da kundin tsarin mulki bayan sanar da mutuwar Shugaba Idris Deby Itno. Amma dai sabuwar majalisar mulkin sojin ta yi alkwarin gudanar da zabe cikin watanni 18 masu zuwa da nufin mayar da kasar ta Chadi kan tafarkin dimukaradiyya.