Tawagar Faransa na ziyara a Aljeriya
October 9, 2022Talla
Wata tawagar gwamnatin Faransa karkashin jagorancin firaminista Elisabeth Borne na ziyarar aiki a Aljeriya, a kokarin gwamnatin Shugaba Macron na bankwana da barakar da ta taba kunno kai a tsakanin kasashen byiu ta hanyar diflomasiyya da bunkasa tattalin arziki.
Wasu daga cikin muhimman batutuwan da suka kai tawagar a Aljeriya har da batun makamashi baya ga huldar kasuwanci, kana shugabar gwamnati Borne da ke samun rakiyar ministoci 16 za ta gana da Shugaba Tebboune a wannan Litinin.